1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Koriya ta arewa zai je Vitenam

Abdourahamane Hassane
February 25, 2019

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un na kan hanyarsa ta zuwa birnin Hanoi na Vietman inda aka shirya zai isa a gobe Talata bayan dogon balaguron da ya yi ta jirgin kasa daga kasarsa zuwa China.

https://p.dw.com/p/3E40S
Nordkorea Kim Yong Un in Flugzeug
Hoto: Reuters/Kcna

Kim Jong Un zai je kasar Vietnam ne domin ganawa da shugaban Amirka Donald Trump a game da batun dakatar da shirin nukiliya na Koriyar. A ganawa ta farko da aka yi a ciki watan Yunin bara tsakanin shugabanin biyu an gaza cimma matsaya, yayin da Anmirka ta bukaci Koriyar ta dakatar da shirinta na nukiliya. Koriyar ta yi shelar cewar ya zama wajibi da farko kasashen duniya su cire mata takunkumin karya tattalin arziki da suka kakaba mata.