1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kira ga daukan matakai kan tsaron Libiya

December 11, 2014

Wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya a yankin Sahel ta sanar a gaban majalisar cewa, tabarbarewar yanayin tsaro a kasar Libiya na babbar barazana ga kwaciyar hankalin Sahel.

https://p.dw.com/p/1E2uT
Syrien-Konferenz in Genf AUSSCHNITT & Symbolbild
Hoto: picture-alliance/dpa

Wakiliyar ta Majalisar Dinkin Duniya Hiroute Guebre Sellassie ta tunatar da yadda aka fuskanci kwararar makammai zuwa sassa daban-daban na yankin Sahel, tare da bunkasar safarar muyagun kwayoyi tun bayan kifar da gwamnatin marigayi Mouammar Kadhafi a shekarar 2011, inda a yanzu kasar ke karkashin jagorancin gwamnatoci biyu da kowanne ke ikirarin cewa shi ne jagora na gaskiya.

Wakiliyar ta kara da cewa a kalla an shigar da makammai dubu 20 zuwa yankin Sahel daga Libiya, kuma mafi yawan muyagun kwayoyi da ake safara, na bi ne ta yankin na Sahel.Tuni dai dama ake rade-radin cewa kungiyar 'yan jihadi ta IS ta girka sansanoni na foras da mutanen ta a kasar ta Libiya, abun da ke kara tayar da hankulla a cewar ta.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Pinado Abdu Waba