1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kirista na yin ƙaura daga birnin Mosul

Christian WalzJuly 19, 2014

Dubban jama'a mabiya addinin Kirista mazauna garin Mosul da ke a arewacin Iraƙi wanda ke cikin hannu masu jihadi na Ƙungiyar ISIS na tserewa daga yankin.

https://p.dw.com/p/1CfQJ
Irak Mosul ISIS Scharia
Hoto: Ammar Mohammed

Jama'ar Kiristan na ficewa ne daga yankin bayan da ya rage sao'i ƙalilan wa'adin ƙarshe da ƙungiyar ta gitta musu domin su Musulunta ko kuma su fice daga garin yake cika a yau Asabar. Kiristocin tare da iyalensu na yin ƙaura zuwa yankin Ƙurdawa mai cin gashin kansa.

Shaidu sun ce tun jiya aka riƙa yin shelar cewar zaɓi ya rage ga Kiristan, ko dai su Musulunta, ko kuma su biya haraji, idan ko ba haka ba sai su fice daga garin. Amirka ta yi Allah wadai da abin da ta kira rashin imani a kan tsiraru mabiya addinin Kirista a Iraƙin da masu kishin addinin ke yi.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Suleiman Babayo