1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kisan gila a kan fararan hula a Sudan ta Kudu

Abdourahamane HassaneFebruary 1, 2016

An ba da rahoton cewar dakarun Sudan ta Kudu sun kashe mutane guda 50 da gangan waɗanda suka bari suka suƙe a cikin wata kontina a cikin watan Oktoba na shekara bara a jihar Uniti.

https://p.dw.com/p/1Hmxu
Südsudan Soldaten Rückeroberung Blue Nile Raffinerie
Hoto: picture-alliance/AA

Rahoton wanda wata hukuma ta ƙasa da ƙasa wacce ke kula da saka ido a kan mutunta yarjejeniyar da aka cimma tsakanin shugaba Salva Kiir da tsohon matamaikinsa Riek MaChar ta bayyana a yau.

Ta ce,ta miƙashi ga ƙungiyar Tarrayar Afirka a lokacin da ta gudanar da taronta a ƙarshen mako a Adis Ababa.a Kasar ta Sudan ta Kudu jami'an tsaro sotari sukan yin amfani da kontina domin kule fursunoni masu laifi ba tare da yin la'akari ba da irin tsananin gumi da ke a cikin kontinar ba.Har ya zuwa yanzu dai gwamatin ta Sudan ta Kudu ba ta ce ufan ba a kan wannan zargi.