1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirikawa na tsokaci kan kisan Suleimani

January 7, 2020

A dai-dai lokacin da Trump yake shirin tura karin dakaru fiye da 3000 zuwa yankin gabas ta tsakiya, Amirkawa na cigaba da yin tsokaci tare da fargabar yiwuwar yaki tsakanin Amirka da Iran

https://p.dw.com/p/3Vq6b
Irak Schiitische Miliz droht USA nach Luftangriffen
Hoto: AFP/H. Hamdani

Kodayake kisan Janaral Soleimani kusan bai zo ma wasu jama‘a da bazata ba, musamman idan aka yi la‘akari da zaman tankiya da ake yi a tsakanin Amirika da Iran, amma ya zuwa yanzu, an gudanar da zanga-zanga fiye da 70 a jihohi daban-daban na Amirka don nuna damuwa kan yiwuwar barkewar yaki a tsakanin Iran da Amirika a sakamakon kashe  Sulaimani.

Yawancin masu zanga-zangar suna dauke da sakwanni da ke cewa, muna son zaman lafiya ba yaki ba, ba ma son a yi yaki domin mai, Amirika ta fice daga Iraqi.

Amirkawa na adawa da yaki kan Iran
Amirkawa na adawa da yaki kan IranHoto: picture-alliance/Zuma Press/C. Sciboz

Dubun-dubatar Amirikawa ‘yan asalin Iran kuwa, ra‘ayoyi sun sha banban,  musamman a tsakanin dattawa da matasa, yayinda tsoffi irinsu Ritass Somani ta yi murna da kashe Janaral Soleimani, wasu matasa irin su Nada Shuaibi kuwa sun ce an yi kuskure

Eric Mitchell, wani tsohon soja ne kuma masanin harkokin tsaro. Ya yi tsokacin cewa, kodayake akwai yiwuwar kasar Iran za ta yi amfani da na‘ura mai kwakwalwa a irin martanin da za ta mayar, akwai bukatar a nan cikin gida, a karfafa matakan tsaro, saboda mai yiwuwa akwai masu tausayawa Iran a nan cikin Amurika, da za su iya kai farmaki.

Zanga znagr Amirkawa a birnin New York
Zanga znagr Amirkawa a birnin New YorkHoto: picture-alliance/dpa/Rainmaker Photo/MediaPunch

Zai yi wuya wani yayi hasashen yadda wannan darga za ta kare tsakanin Iran da Amurika, musanman bisa la‘akari da yadda Shugaba Trump ya kudiri kai farmaki kan wasu cibiyoyin Iran fiye da guda 50, muddin kasar ta dauki matakin rama kisan da aka yi wa Janaral Suleiman, wanda ya zarga da aikata kisa da kuma jin kai sabon farmaki.

Amma jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya Majid Takht Ravanchi ya yi biris da wannan barazana ta Trump, yana mai cewa tabbas Iran za ta dauki fansa.

Yanzu haka dai, shugabar majalisar dokokin Amirika Nancy Pelosi, ta na shirin gabatar da wani kudiri, wanda zai rage ikon Shugaba Trump na yin gaba gadi wajen aiwatar da yaki, tana mai cewa Trump ba zai zama mai mulkin kama karya ba.