1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ta yi tir da wariyar launin fata a Afirka ta Kudu

Uwais Abubakar Idris/ LMJApril 17, 2015

A Najeriya majalisar wakilan kasar ta maida martani mai zafi a kan hare-hare na wariyar launin fata da aka kai a kan bakaken fata a Afirka ta Kudu.

https://p.dw.com/p/1FAHz
Yanayin da ake ciki a Afirka ta Kudu
Yanayin da ake ciki a Afirka ta KuduHoto: picture alliance/dpa/K. Ludbrook

Daga cikin wadanda wannan hari ya shafa dai har da ‘yan Najeriya abinda ya sanya kungiyoyin kare hakkin dan Adam ke yin kashedin hatsarin da ke tattare da hakan. Bakaken fatar Afrika ta Kudu ne dai ke kai wadannan hare-hare a kan ‘yan uwansu bakaken fata da suka kasance a kasar bisa neman abin sakawa a bakin salati wanda ya jefa kasashe da dama cikin mamaki, musamman bisa la'akari da irin gwagwarmayar da kasashen Afirka suka yi musamman Najeriya da ya sanya Afrikan ta kudun kaiwa ga matsayin da ta ke a yanzu.

Majalisar wakilan Najeriya ta yi tir da wariyar launin fata
Majalisar wakilan Najeriya ta yi tir da wariyar launin fataHoto: cc-by-sa/Shiraz Chakera

Wannan ba shine karon farko ba

Munin da wannan hari ya yi dai shekaru uku kenan ana yin irinsa wanda ya sanya majalisar wakilan Najeriyar cewa ba za ta amince da lamarin ba, don haka tai kira ga gwamnatin Najeriyar kan ta dauki mataki. Hon Ahmed Baba Kaita dan majalisar wakilan Najeriya ya bayyana abinda suke son ganin gwamnatin ta yi.

"Na farko tun daga wadancan kashe-kashe da aka yi na wancan lokaci to a biyasu kayan da aka lalata masu, wadanda aka kashe kuma a biyasu diyya, na biyu Afrika ta kudu ta dauki nauyin kare duk wanda ke zaune a kasar ba kawai dan Najeriya ba na uku idan ba'a samu wadannan abubuwa da aka zayyana ba to gwamnatin Najeriya ta kirawo jakadanta da ke Afrika ta Kudu kuma ta kori na nan ya koma kasarsu, har sai an samu matsaya domin ba yau aka fara ba. Kowa ya sani ba abinda ya kai rai daraja a duniya."

Kungiyoyin Kare hakkin dan Adam sun koka

Tuni dai kungiyoyin kare hakin dan Adam suka yi gargadin hatsarin da ke tattare da kai hare-hare na nuna kyama ga duk wani dan Adam, domin ya sabawa kudurorin da suka bada damar walwala da ikon rayuwa musamman hadarin da wannan ke da shi ga yunkurin da aka dade ana yi na samun hadin kan kasashen Afrika da har yanzu ake fafatawa a kai. Mr Kola Banwa jigo ne a kungiyar kare hakkin dan Adam ta Cicilac da ke Abuja ya kuma ce...

Kisan 'yan Afirka a Afirka ta Kudu
Kisan 'yan Afirka a Afirka ta KuduHoto: Reuters/S. Sibeko

"Abinda ya faru a Afirka ta Kudu gaskiya abin damuwa ne domin abu ne da ya shafi hakkin dan Adam. Mutanen nan ba wai sun karya wata doka bane, mutum yana kasuwancinsa sai kawai a taso mashi abin ya zama kowacce shekara sai ya faru. Wannan zai jawa Afirka koma baya domin tun 1963 da aka yi kungiyar hada kan kasashen Afirka OAU ba'a samu ci gaba ba, don an bambanta da yawa a tsakanin kasashen."

Duk da kallon lamarin da ake yi ta fuskar nuna kyama, amma ga Malam Abubakar Ali mai sharhi a kan al'amuran yau da kullum kuma masani a fannin tattalin arziki ya ce duka batu ne na koma bayan tattalin arziki da ya kamata shugabannin Afirka su farka tun kafin lokaci ya kure masu.