Kokari kan yaki da Ebola a Kwango
October 9, 2014Talla
Cikin wata sanarwa da ofishin nasa ya fitar, bayan kammala wata ziyara da ya kai a yankin Boende inda ake fama da wannan cutar da ke a nisan kilo-mita 800 a arewa maso gabacin Kinshasa, wakilin na Majalisar Dinkin Duniya a kasar ta Kongo Martin Kobler, ya ce idan da duk masu hannu cikin lamarin da ma mutanen karkara za su ba da himma tare da bin umarni kamar yadda ake bukata, to da nan da 'yan makonni masu zuwa za a iya shayo kan wannan cuta a wannan yanki.
A cewa hukumar Lafiya ta duniya WHO da ma gwamnatin ta Kwango, cutar ta Ebola a wannan kasa dai ta sha bamban da wadda yanzu haka ke addabar yankin yammacin Afirka, inda ta yi sanadiyar mutuwar mutane kusan 3,900.
Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Suleman Babayo