1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukatar kawo karshen cutar HIV a duniya

Lateefa Mustapha Ja'afarJuly 18, 2016

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci al'ummomin kasa da kasa su tashi tsaye su hada hannu waje guda domin gaggauta shawo kan matsalar cuta mai karya garkuwar jiki, wato HIV AIDs ko kuma SIDA.

https://p.dw.com/p/1JR0K
Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon
Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moonHoto: Reuters/T. Negeri

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniyar ne ya bukaci hakan, inda yace kamata ya yi a jajirce domin tabbatar da dakile cutar kafin nan shekara ta 2030. Rahotanni sun nunar da cewa fiye da rabin al'ummar da ke dauke da wannan cuta a duniya da yawansu ya kai miliyan 37, basa samun magungunan da ke rage radadin ciwon wanda ke taimaka musu wajen samun yin rayuwa mai tsaho. Ban ya bayyana hakan ne yayin taron ranar cutar ta AIDs ko kuma SIDA da ke gudana yanzu haka a kasar Afirka ta Kudu. Wani kiyasi na Majalisar Dinkin Duniyar dai ya nunar da cewa mutane miliyan 17 da ke dauke da cutar ne kawai ke samun magunguna. Al'ummomin kasa da kasa dai na fatan ganin an kawo karshen wannan cuta nan da shekara ta 2030.