1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saudiyya ta ci-gaba da kai hare-hare a Yemen

Lateefa Mustapha Ja'afarApril 23, 2015

'Yan tawayen Houthi na kasar Yemen sun bukaci da a gaggauta kawo karshen baki dayan hare-hare ta sama da kasar Saudiyya ke jagorantar kaiwa a kasar.

https://p.dw.com/p/1FDHy
Hare-haren Saudiya a Yemen
Hare-haren Saudiya a YemenHoto: Reuters

'Yan tawayen na Houthi da ke zaman Musulmi mabiya Shi'a, sun bayyana cewa dakatar da hare-haren shine sharadinsu na shiga cikin tattaunawar sulhu da Majalisar Dinkin Duniya za ta sanya idanu a kai. Rahotanni sun bayyana cewa sa'oi kalilan bayan da fadar mulki ta Riyadh ta bayyana cewa ta kawo karshen hare-haren da ta ke kaiwa a Yemen din, Saudiyyan ta ci gaba da kai hare-hare a kan 'yan Houthi. A cewar jakadan kasar ta Saudiya a Amirka Adel Al-Jubeir tuni suka ci karfin duk wani yunkuri na 'yan Houthi da ma shawo kan barazanar da suke ganin suna yiwa Saudiyya da kan iyakokinta. Ya ce sun tarwatsa sojojin 'yan Houthi na sama da muggan makaman da suke da shi da sansaninsu kana sun lalata mafi yawan kayan aikinsu sun kuma takurasu yadda ba za su iya barin guraren da suke da karfi zuwa wasu sassan kasar ba. Hare-haren da Saudiya ta shafe tsahon wata guda ta na jagorantar kaiwa a kasar ta Yemen dai ya haddasa asarar rayukan fararen hula masu dimbin yawa.