1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin magance kwararar bakin haure daga tushe

Abdourahmane Hassane/SBAugust 11, 2016

Jamus na shirin kaddamar da wani tsari na Plan Marshall da zai taimaka wajen yaki da kwararar 'yan ci rani masu zuwa Turai ta barauniyar hanya daga kasashen Afirka.

https://p.dw.com/p/1Jfxn
Niger Agadez Bild 1 Konvoi mit Migranten verlässt Agadez
Babbar mota dauke da 'yan ci rani a jihar Agadez.Hoto: DW/A. Kriesch/J.-P. Scholz

Bayan kasar Senegal da ya ziyarta, Ministan ma'aikatar hadin kan tattalin arziki da raya kasa na Jamus Gerd Müller, ya ce idan har ana son a kawo karshen lamarin kwararar baki 'yan ci rani galibin su matasa, sai kasashen yammacin duniya sun ba da himma wajen saka jari a nahiyar Afirka na tsawon shekaru da dama.