1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin samar da zaman lafiya a Sudan ta Kudu

Ahmed Salisu RGB
December 4, 2017

Kungiyar TROIKA ta yunkuro don ganin an farfado da yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a Sudan ta Kudu wadda ta shafe shekaru tana fama da tashin hankali tsakanin gwamnati da wadanda ke adawa da ita.

https://p.dw.com/p/2oitn
Afrika Bildergalerie Kindersoldaten im Süd-Sudan
Hoto: DW/A. Stahl

Kungiyar ta TROIKA da ta kunshi Amirka da Birtaniya da Norway ta ce domin ganin kwalliya ta kai ga biyan kudin sabulu ya kamata bangarorin da ke rikici da juna a Sudan ta Kudu su hau kan teburin tattaunawa domin yin gyare-gyare ga yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a cikin watan Agustan shekarar 2015 a kasar Habasha.

Hanzarin kungiyar na neman a yi wa yarjejeniyar gyara shi ne irin sauyin da aka samu musamman a fagen siyasar kasar da ma sauran abubuwa da dama. James David mai sharhi kan harkokin Sudan ta Kudu ya ce baya ga yin gyara ga yarjejeniyar, ya kyautu shugabanni da masu shiga tsakani su fayyace irin rawar da za su taka kan warware matsalar kasar.

A share guda kungiyar TROIKA  damuwa take cigaba da nunawa kan irin halin kunci da al'ummar Sudan ta Kudu ke ciki da kuma halin da tattalin arzikin kasar ya shiga. Wannan ne ma ya sanya suka ga dacewar sake maida hankali wajen sabunta yarjejeniyar zaman lafiya musamman ma batun rabon mukamai da kuma wa'adi na mulki da makamantansu. Wannan damuwa da TRIOKA ke nunawa dai ta sanya Bongiri Peter da ke tsokaci kan lamuran zaman lafiya a kasar cewa dole ne duk masu ruwa da tsaki su tashi haikan wajen ganin sun sauke nauyin da ya rataya a kansu na tabbatar da zaman lafiya a kasar.

Yanzu haka dai masu sanya idanu kan wannan lamari na Sudan ta Kudu na cike da fata na ganin an fidda wani tsari na sanya idanu kan hakikanin abin da ke faruwa da kuma daukar matakai na ganin an kawo karshen halin da kasar ke ciki kana a kyautata 'yancin dan Adam da inganta rayuwar 'yan kasar kana a dafa wajen ganin nan gaba kasar ta kai ga samar da shugabancin da kowa zai aminta da shi.