1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin tallafawa 'yan gudun hijiran Siriya

Kamaludeen SaniFebruary 4, 2016

A wannan Alhamis din nan ce kungiyoyin kasa da kasa gami da wasu kasashen duniya suka hallara a birnin London domin tattara kudaden da za a taimaka wa 'yan gudun hijirar Siriya.

https://p.dw.com/p/1Hq2D
Großbritannien Syrien Geberkonferenz in London Merkel Rede
Hoto: Getty Images/D. Kitwood

Tun dai bayan fada wa halin matsi da neman mafaka a kasashen duniya ciki hadda kasashen kungiyar Tarayyar Turai, 'yan Siriya da ma wasu kasashen yankin gabas ta tsakiya da ke fuskantar tashe-tashen hankula ke cigaba da janyo hankulan kasashen duniya don daukar matsaya guda domin tallafa musu. Majalisar dinkin duniya dai a nata bangaren cewa take muddin ana son a magance matsalolin 'yan Siriyan to akwai bukatar samar da a kalla dala biliyan tara a shekara ta 2016. A yayin bude taron dai shugaban bankin duniya Jim Yong Kim ya yi jawabi...

Großbritannien Syrien Geberkonferenz in London Merkel und Cameron Eröffnung
Hoto: Getty Images/D. Kitwood

Idan muka kiyasta adadin tallafin kudaden da aka baiwa Jordan na biliyan 2.7 a shekara da kuma kasar Lebanon mai dala biliyan 1.6 a shekara a yayin da kuma yanzu muka fahimci yanayin auna mizanin tattalin arzikin kasar Jordan ya sake yin sama, hakan dai ba zai iya dorewa ba.

Ita ma a na ta bangaren Kantomar harkokin kasashen wajen kungiyar Tarayyar Turai Federica Mogherini bayan ta bayyana irin tallafin da kungiyar za ta bai wa 'yan Siriyan nuni tayi da cewar:

"Kudade ba su ne za su magance matsalar 'yan Siriya ba kun fini sanin haka. Idan kana da kudi kana kuma samun taimakon agajin jin kai, bayan baka da walwalar harkokin siyasa aikin tamkar aikin baban giwa ne, zamu sake haduwa ne a shekara mai zuwa tare da neman karin kudade ba tare da an tsinana komai ba wajen warware matsalar."

Federica Mogherini auf der Geberkonferenz für Syrien in London
Hoto: Reuters/T. Melville

Shi kuwa daga nashi bangare Firaministan kasar Turkiya Ahmed Davutoglu cewa yake.

"A yau Turkiya ta karbi bakunci 'yan gudun hijirar Siriya sama da miliyan biyu wanda shine irin sa mafi girma a duniya da wata kasa ta karbi 'yan gudun hijira, kananan yara 'yan Siriya dubu 700 na makaranta a Turkiya, babu wani birni a Turkiya da babu 'yan gudun hijiran Siriya."

A yayin taron dai, kasashe da suka hada da Jamus da Amirka da Biritaniya da Faransa da Norway da Italiya da Saudiya da Hadaddiyar Daular Larabawa, na a kan gaba wajen bayar da tallafin kudade masu tsoka don tallafawa dumbun masu gudun hijirar kasar Siriya baki daya.