1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mali: Sanya hannu kan yarjejeniyar sulhu

Lateefa Mustapha Ja'afarMay 15, 2015

A kasar Mali ana bikin sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ta din-din-din tsakanin gwamnati da kungiyoyin 'yan tawayen kasar.

https://p.dw.com/p/1FQRq
Hoto: REUTERS/Souleymane Ag Anara

Sai dai babbar kungiyar hadaka ta 'yan tawayen kasar "The Coordination of Azawad Movements" (CMA) da ke fafutukar ganin samun 'yancin kan yankin Abzinawa ta sanar da cewa ba za ta halarci bikin na Bamako babban birnin kasar ta Mali ba. Tuni dai shugaban kasar Zimbabuwe Robert Mugabe wanda kuma shine shugaban kungiyar Tarayyar Afirka AU ya isa birnin na Bamako yayin da ake sa ran halartar akallah shugabannin kasashen nahiyar Afirkan 20 wajen wannan biki. Bikin dai ya biyo bayan kwashe tsahon watanni da Majalisar Dinkin Duniya ta yi tana shiga tsakani domin tabbatar da ganin an samu zaman lafiya mai dorewa a kasar ta Mali.