1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin warware rikicin Iraki a siyasance

June 23, 2014

Kungiyar tarayyar Turai ta EU da Amirka na kokarin bin hanyoyi na diflomasiyya wajen ganin an kawo karshen tada kayar bayan da 'yan kungiyar nan ta Sunni ta ISIS ke yi a Iraki.

https://p.dw.com/p/1COKM
Bildergalerie ISIS
Hoto: Getty Images/Afp/Ahmad Al-Rubaye

Kungiyar ta tarayyar Turai na duba wannan batu ne a wani taro da ministocin harkokin wajen mambobinta ke gudanarwa a kasar Luxembourg. Kungiyar ta ce ta damu matuka dangane da yanayin da Irakin ke ciki musamman ma cigaba da kame yankuna da biranen da 'yan ISIS ke yi.

EU din da kasashen yammacin duniya dai na ganin muddin ba a gaggauta magance wannan matsala ba to kuwa za ta bazu zuwa sauran sassan kasar da ma kasashen da ke makotaka ta da ita. Wannan ne ma ya sanya sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry ya shirya wata ziyara ta ba zata zuwa Irakin don tataunawa da Firaminista Nuri al-Maliki da nufin shata hanyoyin warware rikicin.

To sai dai ana ganin da kamar wuya a iya cimma wani abu kwakkwara don a baya Amirka ta nemi al-Maliki da ya yi murabus a wani mataki na farko na kashe wutar rikicin, matsayin da gwamnatin Irakin ba ta yi na'am da shi ba. Wannan ne ma ya sanya Ayatoullah Khameni cewar ba sa maraba da sanya bakin Amirka kan rikicin.

U.S. Außenminister John Kerry und Nuri Al Maliki Premierminster Irak 23.06.2014 Bagdad
John Kerry da Nuri al-Maliki na kokarin warware rikicin IrakiHoto: REUTERS

Ya ce ''muna matukar adawa da tsoma bakin Amirka da sauran kasashe kan harkokin cikin gida da suka shafemu. Sam ba za mu amince da haka ba don mun yarda cewar gwamnatin Iraki da al'ummar kasar gami da shugabannin addinai za su iya kawo karshen wannan rikici da yardar Allah''.

To sai dai yayin da Ayatoullah Khameni ke ganin cewar ba su bukatar tsoma bakin kasashen ketare wajen warware wannan tada kayar bayan da mayakan ISIS din da ke bin tafarkin Sunna ke yi, Neils Annen kakakin jam'iyyar SPD da ke kula da harkokin kasashen ketare a majalisar dokokin Jamus ta Bundestag na da akasin wannan tunani, inda ya ke cewar kyautuwa ya yi a ce kasashen duniya sun dafa sannan kuma a nemi hanyoyin warware rikicin ta hanyoyi na siyasa.

Irak Schiiten-Miliz in Bagdad
Mayaka 'yan Shi'a na cigaba da dafawa gwamnatin Iraki wajen yakar 'yan ISISHoto: MOHAMMED SAWAF/AFP/Getty Images

Ya ce ''muna bukatar wata mafita ta siyasa. Ya na da kyau a hau teburin tattaunawa da bangarorin da ke rikici da juna don fidda hanyoyin warware rikicin. Ina ga ba wani mataki da ya wuce haka.

A daura da wannan yunkuri da ake kokarin yi na warware rikicin na Iraki musamman ma dai ta hanyoyi na diflomasiyya, rahotanni daga kasar na cewar mayakan ISIS na cigaba da kame wurare masu muhimmanci, na baya-bayan nan dai shi ne filin jirgin saman Tal Afar wanda mai magana da yawun firaministan kasar ta fannin tsaro Laftanar Janar Qassem Atta ya ce ya yanzu ya fada hannun 'yan ISIS din.

Abin jira a gani dai yanzu haka shi ne irin tasirin da matakan jami'an diflomasiyyar kasa da kasa za su yi wajen kashe wutar rikicin da ma irin kokarin da gwamnatin kasar za ta yi don ganin an zauna lafiya.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammad Nasiru Awal