1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin zaman lafiya a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Suleiman BabayoMay 11, 2015

Mahalarta babban zaman taron sasantawa da ya gudana a birnin Bangui, sun amince da rattaba hannu kan samar da zaman lafiya da tsaro, tare da ajiye makammai.

https://p.dw.com/p/1FOAC
Catherine Samba-Panza
Catherine Samba-PanzaHoto: Reuters

Lokacin da aka bai wa mutane na mahawara yayin zaman tattaunawar duk da cewa ya yi kadan, amma taron ya tsayar da abubuwa masu mahimmanci, inda yayin taron an kafa kwamitoci da za su kula da mahimman ayyuka gwamnati. An amince da tsawaita lokacin da za a yi zabe, sannan za a tuntunbi shugabanin kasashe na kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen tsakiyar Afirka domin samun amincewarsu kan yadda shugabannin gwamnatin rikon kwarya zasu ci gaba da rike madafun iko zuwa lokacin zabe duk da cewa wa'adin mulkinsu ya kawo karshe a fannin doka. Joseph Bindoumi ya kasance mamba a kungiyoyin fararen hula na kasar ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya inda yake cewa:

Mahimmancin dage lokutan zabukan kasar.

"Matsala a fannin yanayin, da tsaro, sannan ga matsalar rashin kudi sun nunar cewa zai yi wuya a yi zabe a watan Yuli zuwa Agusta mai zuwa. Amma duk da haka zaben dole za a yi cikin wannan shekara ta 2015. Abu na biyu shi ne ya kamata ace mulkin rikon kwarya ya kawo karshe, amma da yake wannan matsala ta zo hukumomin rikon kwarya za su ci gaba da rike madafun iko har zuwa lokacin da za a shirya zabukan kasa."

Zentralafrikanische Republik Medien
Hoto: SIA KAMBOU/AFP/Getty Images

A lokacin zaman taron kimanin kungiyoyi 10 ne suka saka hannu kan yarjejeniya zaman lafiya, inda suka amince da watsi da makamai nan take. Babban abin da yanzu aka saka gaba shi ne tabbatar da adalci da sake hada kan 'yan kasa, kamar yadda wasu daga cikin mahalarta taron membobin kungiyoyi masu dauke da makamai ke nuna amincewarsu.

François Bozizé da Michel Djotodia
François Bozizé da Michel DjotodiaHoto: AFP/Getty Images/S. Jordan

Kungiyoyin mayaka sun amince da ajiye makammansu.

"Yau ta zama rana ta karshe kan wannan tattaunawa a gaskiya muna cike da fatar cewar za a samu abin da ke nema musamman a fannin dorewar zaman lafiya a wannan kasa. Mun zo cikin yanayi na yafe wa juna domin samun zaman lafiya."

"Abin da yasa muka zo nan shi ne domin kowa yana bukatar samun zaman lafiya a wannan kasa. Tun da dama ce a gare mu yadda za a binne makaman yaki don ci-gaban kasarmu, domin saka wannan hannu ya nuna kowa ya amince da zaman lafiya bayan taro."

Ana fata wannan taron sulhu ya kawo karshe rikicin fiye da shekaru biyu da kasar ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya take ciki, abin da ya janyo tura jadarun kasar Faransa gami da dakarun kiyaye zaman lafiya 10,000 karkashin Majalisar Dinkin Duniya. Shugaba Catherine Samba-Panza ce dai ke jagorancin gwamnatin ta rikon kwaryar kasar.