1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koma baya ga bakuncin taron G8 da Rasha za ta karba

March 3, 2014

Kasashe bakwai daga cikin takwas na G8 sun soke halartar taron da za su yi a Sochi na Rasha.

https://p.dw.com/p/1BISR
Nordirland Treffen Obama Putin G8 2013
Hoto: Reuters

Kungiyar kasashe bakwai da ke da karfin tattalin arziki a duniya na G7, ta soke shirye shiryen halartar taron Kungiyar G8 da ke da karfin masana'antun, wanda dama suka shirya gudanarwa a birnin Sochi na kasar Rasha, ranar takwas ga watan Yuni. Wannan matakin, na zama martani ne ga matakan da Rashar ta dauka a Yukren. A birnin Washington na Amirka ne, fadar shugaban kasar ta White House ta fitar da wata sanarwa - a madadin shugabannin kasashen Kanada, da Faransa, da Jamus ,da Italiya. Sai kuma Japan, da Birtaniya da kuma ita kanta Amirka, game da Kungiyar Tarayyar Turai. Hakanan sanarwar ta yi Allah wadai da tarayyar Rasha game da kutsen da ta yi ga 'yancin kasar Yukren, kana ta bukaci tallafawa kasar ta Yukren domin farfado da tattalin arzikinta.

Mwallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mohammad Nasiru Awal