1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zangar adawa da mujallar Hebdo

January 16, 2015

Akalla mutane biyu ne suka rasa rayukansu yayin da wasu da dama suka jikkata a lokacin gagarumar zanga-zangar da wasu mabiya addinin Musulunci suka shirya a birnin Damagara.

https://p.dw.com/p/1ELvZ
Hoto: DWM. Kanta

An dai shirya wannan zanga-zanga ne domin nuna adawa da sake wallafa zanen batanci ga Fiyayyen halitta Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, da mujallar Charle Hebdo ta yi. Wakilinmu na birnin Damagaram din Larwana Malam Hami ya ruwaito cewa wasu masu tsattsauran ra'ayi sun kona cibiyar al'adun kasar Faransa da ke birnin na Damagaram da kuma coci-coci da shaguna a yayin wannan zanga-zanga. Kawo yanzu dai babu wata kungiya da ta bugu kirji ta bayyana cewa ita ta shirya wannan zanga-zanga. Masu zanga-zangar da ta juye ta zama rikici dai sun yi arangama da jami'an tsaro dauke da makamai da suka yi amfani da hayaki mai sa hawaye a kokarin tarwatsa su.

Mawallafa: Larwana Malam Hami/Lateefa Ja'afar

Edita: Mohammad Nasiru Awal