1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Korafin 'yan Nijeriya kan rabon katin zabe

August 18, 2014

Wasu jihohi goma na Najeriya sun gamu da cikas a kokarin raba katin zabe, abinda ke janyo korafi na masu karbar katin har ma da mambobin jam'iyyun adawan kasar.

https://p.dw.com/p/1CwUs
Wahlen Nigeria Attahiru Jega
Attahiru Jega shugaban hukumar zaben NajeriyaHoto: AP

A Najeriya aikin ba da katin jefa kuri'a na dindindin a wasu jihohi har da Abuja na gamuwa da cikas abin da ya haifar da koke-koke daga masu karbara katin dama jam'iyyun siyasa duk da kara wa'adin kwanaki biyu na karabar katin a wurin da aka yi rijista da hukumar zaben ta yi.

Daukan dogon lokaci ba tare da samun kai wa ga katin ba ga mutane da dama a rana ta biyu ke nan suna jerangiya ya sanya bayyana bacin ransu a kan abin da suke ganin ya kamata a ce sun samu a tsanake, kamar yadda wasu daga ciki suka bayyana.

Wahlen Nigeria Stimmabgabe Wahllokal
Hoto: dapd

Zargin rashin tsari da cunkusa na jama'a a runfa guda ya haifar da wannan matasala wajen karbar katin da ya tilasta wa hukumar zaben Najeriyar karin wa'adin kwanaki biyu domin kafin daga bisani a ci gaba da ba da katin a ofishin hukumar zabe na kanana hukumomin kasar. Dr Sadeeq Umar Abubakar sakataren gudanarwa na jamiyyar adawa ta SDP ya bayyana korafin cewa duk wadanann matsaloli ne da sun ja kunen hukumar zaben ganin an fuskaci irinsu a jihohin Osun da Ekiti.

Hukumar zaben ta kara jaddada cewa duk wanda bai samu wannan sabon katin to ba zai samun damar yin zabubbukan 2015 da ke tafi. Abin jira a ganin ko sabon katin da aka tsara shi da daukar hoton ‘yan yatsu zai taimaka rage magudin zabe da ke zama kalubale ga shirya zabe a Najeriya.

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris (daga Abuja)
Edita: Suleiman Babayo