1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koriya ta Arewa ta gargadi China

Abdul-raheem Hassan
May 4, 2017

Koriya ta Arewa ta ja kunnen babbar kawarta kasar China da ta bi sannu a hankali dan gudun bacin rana. A wani shirin talabijin na musamman Koriya ta ce China ta godewa Allah da kyakkyawar dangantaka da ke tsakanin su.

https://p.dw.com/p/2cK4j
Nordkorea Kim Jong-un
Hoto: Reuters/KCNA

Gargadin ya ci gaba da cewa China ta bi sannu kuma ta kwana da sanin ramin maciji bai gaji zungura ba, a cewar Koriyar dai idan China ba ta dena katsalandan a harkokinta ba, to kasar za ta dandana kudarta. Ba dai kasafai ake ji tsakanin kasahe da ke cin moriyar juna ta fuskokin kasuwanci ba amma a baya bayannan Amirka na matsawa China lamba dan takawa Koriyar birki kan sarrafa makaman Nukiliya. Amirka dai na kalubalantar aniyar Koriya ta Arewa na ci gaba da gwada makaman Nukiliya to amma duk da matsin lamba da Koriyar ke sha daga sauran takwarorinta, a baya-bayannan ta sanar da cewa ta na dab da sake gwada wani makamin na Nukiliya.