1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koriya ta Kudu ta koma farfagandar kan iyaka

Gazali Abdou TasawaJanuary 8, 2016

Koriya ta Kudu ta koma a wannan Jumma'a gudanar da farfaganda da take yi da manyan Lasifikoki kan iyaka da takwararta ta Arewa a matsayin martani ga gwajin makamin nukliya da Koriya ta Arewar ta gudanar.

https://p.dw.com/p/1Ha5M
Südkorea Lautsprecher Propaganda
Hoto: Getty Images/Chung Sung-Jun

Koriya ta Kudu ta koma a wannan Jumma'a gudanar da farfaganda da take yi da manyan Lasifikoki kan iyaka da takwararta ta Arewa a matsayin martani ga gwajin makamin nukliya na baya-bayan nan da Koriya ta Arewar ta gudanar.Koriya ta Kudu ta koma gudanar da farfagandar ce, wacce ga al'ada ke bakanta wa hukumomin Koriya ta Arewa da rai a wannan rana ta zagayowar cikon shekaru 32 da haifuwar Shugaban Koriya ta Arewar Kim Jong-Un.

A cikin watan Agusta na shekarar bara ne hukumomin Koriya ta Kudun suka kwance lasifikokin farfagandar tasu a sakamakon wata yarjejeniyar neman sasanta kasashen guda biyu da suka kusa kai ga gwabza fada a sakakamakon wannan farfaganda ta kan iyaka.