1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu a Burundi ta amince da takarar shugaban kasar

Yusuf BalaMay 5, 2015

A ranar Talatan nan ma dai masu zanga-zangar sun dunfari ofishin jakadancin kasar Amirka amma 'yan sanda suka tarwatsa su.

https://p.dw.com/p/1FKRh
Burundi Kandidatur des Präsidenten
Hoto: Getty Images/AFP/P. Moore

Kotun da ke lura da harkokin da suka shafi sha'anin tsarin mulkin kasar Burundi ta amince a ranar Talatannan cewa shugaban kasar na da damar sake neman tsayawa takara a zaben kasar da ke tafe, takarar da ta kasance mai cike da cece-kuce da ta sanya shi kansa mataimakin shugaban kotu ya tsallake daga kasar da bayyana hukunci da cewa bai halatta ba.

Wannan hukunci dai ya fito ne bayan lokaci da aka dauka ana gudanar da zanga-zangar adawa da tazarcen na shugaba Nkurunziza.

A wata kididdiga da ofishin kungiyar bada tallafin gaggawa na Red Cross ya fitar a birnin na Bujumbura na Burundi akalla mutane tara sun rasu a fafatawar da aka yi tsakanin masu zanga-zangar da 'yan sanda yayin da wasu da dama suka sami raunika.