1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu ta buƙaci da a yanke wa Mohamed Mursi hukuncin kisa

Abdourahamane HassaneMay 16, 2015

Kotun a Masar na zargin tsohon shugaban ƙasar da laifin yi fashi na wani gidan kaso a shekaru 2011 tare da wasu magoya bayansa.

https://p.dw.com/p/1FQj4
Ägypten Mursi Urteil
Hoto: picture alliance/AP Photo/T. el-Gabbas

Wata kotu a Masar ta buƙaci da a zartas da hukuncin kisa ga tsohon shugaban ƙasar Mohamed Mursi,tare da wasu ɗaruruwan 'yan Ƙungiyar 'Yan uwa Musulmi waɗanda ake zargi da hannu a fasa wani gidan kurkuku da 'yan kaso suka tsere a lokacin juyin-juya hali na shekara ta 2011.

Kotu ta nemi kuma da a yanke hukuncin na kisa ga jagoran Ƙungiyar ta 'Yan Uwa Musulmi Khairat El Shater tare da wasu mutane 15 saboda hada baki da wasu jami'an na ƙasashen waje domin tada fitina a cikin ƙasar.