1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yanke hukunci dauri kan tsohon Firaministan Pakistan

July 6, 2018

Wata kotun mussamman ta yaki da cin hanci ta tura Nawaz Sharif tsohon Firaministan kasar Pakistan gidan yari na tsawon shekaru goma.

https://p.dw.com/p/30y4j
Premierminister Pakistan Nawaz Sharif
Tsohon Firaministan Pakistan Nawaz ShariffHoto: picture-alliance/dpa

 

Kotun ta ce da shi da iyalansa sun gaza bayar da bayanin yadda sun ka tara dukiyar da su ka sayi gidaje na alfarma a birnin landan na Birtaniya. Kuma sun gaza fayyace wa hukumomin haraji na kasar pakistan, yadda aka yi suka tara kadarorinsu da ke Pakistan. A don haka ne ma kotun ta tura diyarsa mai suna Maryam Nawaz gidan yari na shekaru bakwai. Baya ga wannan zargin dai, sunan diyar Nawaz Sharif ya fita a cikin jerin mutanen da suke almundahanar kudade a duniya da aka fi sani da Panama papers.

Yanzu haka dai tsohon Firaiministan ya na landan. Amma lauyoyi sun ce zai iya daukaka wannan hukunci da kotun ta zartar a yau juma'a.

Wannan hukunci dai shi ne hukunci na farko da aka zartar a jerin tuhume-tuhume da ake zargin tsohon firaministan. A shekarar da ta gabata ne dai kotun kolin kasar ta Pakistan tunbuke shi daga karagar mulki.