1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu ta yi watsi da belin 'yan adawa a Zimbabwe

March 20, 2013

Alkalin wata kotu a Zimbabwe, ya ki amincewa da bukatar belin magoya bayan praministan Tsvangirai a bisa dalillin yawan laifufukan da ake zargin su da aikatawa.

https://p.dw.com/p/180zz
Hoto: AP

A wani zaman da kotu ta yi a birnin Harare na Zimbabwe, Alkalin kotun ya yi watsi da bukatar belin magoya bayan Morgan Tsvangirai da su da lauyoyin da ke kare su. A makon da ya gabata ne jami'an tsaro suka cafke wasu magoya bayan praministan sannan daga bisani kuma aka cafke lauyoyin da ke musu kariya.
Kotun ta bayyana daukar matakin na watsi da bukatar sallamar su ne, a dangane da tarin laifufukan da ake zargin su da aikatawa, musamman na cin amanar kasa. Daga cikin wadanda aka cafke har da wani na hannun damar Tsvangirai a kan zargin yunkurin kisa.
Rikici dai ya barke ne tsakanin bangaren shugaba Robert Mugabe da na praminista Morgan Tsvangirai a lokacin yakin neman zaben raba gardaman da aka yi a makon jiya.

Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Zainab Mohammed Abubakar