1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotun ECOWAS ta ce gwamnatin Najeriya ke laifi

Usman ShehuDecember 17, 2012

Gwamnatin Najeriya ke da laifi bisa gurɓacewar mallahi a yankin Niger Delta, inji kotun ECOWAS

https://p.dw.com/p/1741d
In this June 20, 2010 photo, men stand in an oil slick covering a creek near Bodo City in the oil-rich Niger Delta region of Nigeria. As U.S. officials now work to stanch the flow from the Gulf Coast spill, Nigeria remains mired in spills after 50 years of production by foreign firms eager for the country's easily refined fuel. Environmentalists estimate as much as 546 million gallons of oil have spilled into the country's Niger Delta during that time, roughly at a rate comparable to one Exxon Valdez disaster per year. (ddp images/AP Photo/Sunday Alamba).
Mai da ya mala a yankin Bodo, OgoniHoto: AP

Ƙungiyoyin kare haƙƙin jama'a sun jinjinawa hukuncin da kotun al'ummar yankin Afrika ta yamma wato ECOWAS ta yanke, inda ta umurci gwamnatin Najeriya da ta tilastawa hukunta kamfanonin man da suke gurbata muhalli a yankin Niger Delta mai arzikin mai a kasar.

Wannan hukunci da ake wa kallo mai cike da tarihi a fafutukar da aka dade ana ci gaba da yi don shawo kan matsalolin gurbata muhalli a yankin Niger Delta mai afrzikin man fetur, wanda matsalolin gurbacewar muhalli ke ci gaba da jefa rayuwar al'ummar yankin cikin mawuyacin hali.

A photograph made available 19 August 2010 shows the Chevron oil facility under contruction in Escravos, 56 miles from Warri in the oil rich Niger delta region of Nigeria 17 August 2010. Nigeria is the fifth largest exporter of oil to the United States and the largest producer of oil in Africa. For decades, thousands of spills across the fragile Niger Delta have hampered the livelihoods of fishermen and farmers, contaminated water sources and polluted the ground and air. Approximately 300 spills are estimated each year. Some are small and some are continuous leaks but compounded they continue to pollute the delta. EPA/GEORGE ESIRI Schlagworte Fabrik, Erdöl, düster, Ufer, Wolken, Schiff, dunkel, Öl, Wirtschaft, Himmel, Schiffe, Natur, Industrie, Verkehr, Unternehmen, Gewässer
Matatar mai a yankin Niger DeltaHoto: picture-alliance/dpa

Kotun ta Ecowas da hakkake cewar gwamnatin Najeriyar ta karya dokar kuduri ta 21 na yancin rayuwan kasashen Afrika da kuma kuduri na 24, bisa gazawarta wajen kare al'ummun yankin Niger Delta daga ayyukan kamfanonin mai da suka gurbata masu muhallin. To ko wace hanya  wannan ya shafi batun take hakkin jama'a da masu fafutuka a wannan fannin ke danganata shi da gurbata muhallin? Malam Alhassan Mahmoud na kungiyar kare hakin jama'a da tsaron kasa na cikin masu fafutuka a kan wannan lamari.

"Wannan hukunci da kotun ECOWAS ta yi abinda ya nuna shine akwai abubuwan da ya kamata a yi wa bil-Adama da ba'a yi ba. Ba ma a yankin Niger Delta kadai ba don abin da ya sa duniya ta san nasu don suna da mai ne da ake samun malalewarsa, to don haka akwai sauran wurare a Najeriya da ake fama da wannan matsala kaman in ka duba misali Kainji inda ake samar da wutar lantarki ba wai ga Najeriya kadai ba" 

A file picture dated Friday 17 September 2004 of the body of a dead Nigerian man in the mud in front of a column of smoke rising from an exploded pipeline after oil smugglers tried to cyphon off oil in Lagos, Nigeria where more than 40 were killed on . The oil price broke the 50$/barrel rate Tuesday 28 September 2004. One of the reasons being cited is the ongoing rebelion in Nigeria's oil rich delta region where local malitia have cripled Nigeria's 2.3 million barrels per day output. Nigerian rebels fighting for sovereignty of the oil-producing Niger delta have told oil companies, Royal Dutch Shell Group, Nigeria's largest oil producer, and Italy's Agip, to shut production before they begin an 'all-out war' on 01 October 2004. Nigeria is the world's seventh largest exporter of oil. dpa
Wani butun mai ke cin wuta a yankin Niger DeltaHoto: picture alliance/dpa/dpaweb

Batun gurɓacewar muhalli da ake zargin kamfanonin da ke hako mai a yankin Niger Delta dai lamari ne da aka dade ana ja in ja a kansa musamman ganin lamari ne da kwararru suka bayyana illarsa ga rayuwar alummar yankin saboda yadda yake gurbata ruwa, iska da ma kasar noman da suka dogara a kanta.

Tuni wannan ya haifara da tada jijiyar wuya a tsakanin alummun yankin da ma kungiyoyin kare hakkin jama na cikin Najeriyar da kasashen ketare abinda ya sanya Chief Asara Sinos na yankin Niger Delta da ke cikin wadanda suke fafutukar wanna lamari bayyana cewa.

An aerial view shows an oil spill which pollutes a waterway 30 March 2003 in Nigeria's Niger Delta near the Escravos export terminal. The troubled region's oil facilities have been closed down and evacuated during two weeks of bloody ethnic violence. Foto: Pius Utomi Ekpei dpa
Mai ke mala cikin ruwa a yankin Niger DeltaHoto: picture alliance/dpa

Yace "abinda muke cewa shine gwamnati ta bamu muhallinmu ta gyara shi ya kasance mai tsafta, amma in gwamnati na ci gaba da nuna rashin kulawa to ba za mu lamunci hakan ba"

An daɗe ana kokarin tankwasa gwamnatin Najeriyar ta dauki mataki a kan irin wadannan laifuffuka na gurbata muhalli ba tare da samun wani ci gaba.

Domin har zuwa wannan lokaci ana ci gaba da jan in ja a tsakanin gwamnatin Najeriya da kamfanion Shell a game da aikin share gurbataccen man da ya malala a yankin Ogoni na Niger Delta.

Abin jira a ganin shine matakin da gwamnatin Najeriyar za ta dauka a kan wannan hukunci na kotun ta ECOWAS.

Mawallafi: Uwaisu Abubakar Idris

Edita:       Usman Shehu Usman