1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotun kolin Kenya ta yanke hukunci kan zaben 4 ga watan Maris

March 30, 2013

A dazu-dazun nan ne rahotanni daga Nairobi suka bayyana cewar kotun kolin kasar Kenya, ta bayyana Uhuru Kenyatta a matsayin mutumin da ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar makwani 3 da suka gabata

https://p.dw.com/p/187Ig
Hoto: Reuters

Dama dai a wannan Asabar ce kotun za ta duba karar da abokin hamayarsa wato Raila Odinga ya shigar a zargin da ya yi na an tafka aringizon kuri'u a zaben da aka gudanar.

Da ya ke karanta sakamakon zaman da suka yi babban alkalin kotun Willly Mutunga ya ce bisa ga binciken da suka gudanar tun lokacin da aka gabatar musu da kara, shaidun da suka tattara sun bayana musu cewa an gudanar da sahihin zabe, don haka sun yake shawarar cewar babu maganar satar kuri'u.

Jim kadan bayan sakamakon kotun Raila Odinga ya kira magoya bayansa da su mutunta hukuncin tare da taya abokin hamayarsa wato Uhuru Kenyatta murna da kuma yi masa fatan alheri a jagorancin da zai yi wa kasar.

Shi dai Uhuru Kenyatta na daga cikin wadanda kotun hukunta manyan laifufuka ta kasa da kasa ke zargi da hura wutar rikicin da ya barke a kasar biyo bayan zabukan da aka yi a shekara ta 2007

Mawallafi: Issouhou Mamane
Edita: Halima Balaraba Abbas