1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kuba za ta maido da huldar diplomasiyya da Amirka

Mohammad Nasiru AwalDecember 17, 2014

To sai dai har yanzu ba a warware muhimmin batun nan na takunkumin karya tattali arziki da Amirka ta kakaba wa Kuba tun shekarar 1960.

https://p.dw.com/p/1E6WH
Soweto Handschlag Castro Obama Beerdigung Mandela 10.12.2013
Hoto: picture alliance/AP Photo

Shugaban kasar Kuba Raul Castro ya ce kasarsa ta amince ta maido da huldar diplomasiyya da kasar Amirka bayan wata musayar firsina ta share fagen samun wannan ci gaba na tarihi. Sai dai Castro ya ce hakan ba ya nufin an warware babbar matsalar da ke akwai wato takunkumin karya tattalin arziki da Amirka ta sanya wa kasar tun a shekara ta 1960.

Shugaba Castro ya kuma yaba wa shugaban Amirka Barack Obama dangane da matakan da ya dauka na maido da dangantaka da Kuba bayan kwashe shekaru fiye da 50 ana zaman doya manja. Da farko dai Shugaba Obama ya nuna cewa lokaci ya yi da za a dawo daga rakiyar tsoffin manufofin Amirka kan Kuba.