1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kundin tsarin demokradiyya na Magna Carta

Gazali Abdou TasawaJune 15, 2015

A ranar 15 ga watan Yuni na shekara ta 1215 Sarki John na Ingila a karo na farko ya gabatar da wannan kundi a wani mataki na hana barkewar yakin basasa a kasarsa.

https://p.dw.com/p/1FhY2
Großbritannien Queen Elizabeth und Cameron beim Magna Carta 800. Jubiläum
Hoto: Reuters/C. Jackson

Ingila da ake wa lakabi da uwar kwallon kafa, ta kasance uwar sabon tsarin demokradiyya da mulki na doka, wanda aka tattara cikin wani kundi da a ranar 15 ga watan Yunin 2015, ya cika shekaru 800, wato kundin Magna Carta. Har yanzu kuwa tsarin mulkin Birtaniya ya kunshi wasu sassa uku da suka samo asali daga kundin na Magna Carta. Shin me wannan kundi na tarihi ke nufi? Wace irin rawa ta tarihi ya taka tsawon wadannan shekaru? Mohammad Nasiru Awal na dauke da karin bayani.

A ranar 15 ga watan Yunin shekarar 1215 aka yi wani taro tsakanin sarkin Ingila John da wakilan 'yan gwagwarmayar neman 'yanci da ke adawa da tursasawar da ke musu musamman na kudi haraji mai yawa. Don hana barkewar wani yakin basasa, Sarki John ya albarkaci wani kundi da ke zama wata yarjejeniyar zaman lafiya. A karon farko a Ingila wannan kundi ya tanadi kare hakin jama'a. David Carpenter farfesan tarihi ne a King's College da ke birnin London ya yi kari haske game da kundin na Magna Carta.

Bill of Rights England 1689
Hoto: picture-alliance / KPA/TopFoto

Ya ce: "Sabon kundin da ke zama wani ginshikin juyin juya hali shi ne hatta shugaba na karkashin doka. Muhimmin abu ga kundin shi ne bayanai dalla-dalla da ke ciki wanda kuma ya sa ya shahara a duniya, amma wadanda suka zo gabaninsa ba su yi irin wannan tasirin ba."

Abubuwan da ya kunsa sun kasance sabbi, wato yi wa masu laifi adalci a gaban shari'a, ba za a jefa mutum kurkuku ba da tare da kotu ta yanke masa hukun ci ba, duk mai biyan haraji zai samu wakilci.

Yanzu haka dai ba kundin Magna Carta sai wasu bangarori na kalmominsa na asali.

Tun a karni na 17 wannan kundin na Magna Carta ke samun karbuwa inda ya zama wani abin koyi da al'umma ke ba sa sabuwar fassara. Alal misali ya zama ginshikin dokar kare hakkin jama'a a Birtaniya a shekarar 1689 da yarjejeniyar Faransa kan 'yancin dan Adam da aka kulla shekaru 100 baya da kuma yarjejeniyar kare hakkin dan Adam ta shekarar 1948, an shigar da shi cikin kundin tsarin mulkin Amirka, inji Heather Rowland ta hukumar adana kayan tarihi ta birnin London.

Großbritannien Verfassung Magna Carta
Hoto: picture-alliance / dpa

Ta ce: "Ya zama muhimmin abu musamman ma a kasar Amirka, inda aka yi amfani da shi kuma aka shigar da shi cikin kundin tsarin mulkin Amirka. Abin mamaki ne da wannan kundin na Ingila ya shiga cikin kundin tsarin mulkin kasashe da dama a duniya, amma kuma har yanzu ba mu da shi a matsayin rubutaccen kundi."

Shi ma dan gwagwarmayar neman 'yancin kasar Indiya Mahatma Ghandi da ya nema wa kasar 'yancin kai a shekarar 1947 ya mayar da hankali kan kundin na Magna Carta. Haka shi ma garzon neman 'yancin kasar Afirka ta Kudu Nelson Mandela ya rawaito wasu sassa na kundin lokacin masa shari'a a shekarar 1964. Har yanzu wannan kundi da ya samo asali daga shekarar 1215 na zama wani ginshiki na 'yanci da walwala da kuma mutunta hakin dan Adam.