1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'yan gudun hijira za su rabauta da sana'oi a Najeriya

Zulaiha Abubakar
September 12, 2019

Shugaban kungiyar agaji ta Red Cross Peter Maurer ya bayyana cewar kungiyar ta shirya don samar da hanyoyin samun kudaden shiga a yankunan da suka yi fama da tashe-tashen hankula.

https://p.dw.com/p/3PVNg
Peter Maurer
Hoto: Reuters/D. Balibouse

Mista Maurer ya bayyana haka a wata ganawa da ya yi da masu masana'antu da 'yan kasuwa a jihar Lagos da ke tarayyar Najeriya a wannan rana ta Alhamis.

Yankunan da kungiyar ta zaba don fara gwajin wannan al'amari sun hada da jihohin da rikici ya raba al'umma d muhallansu da sansanin 'yan gudun hijira da kuma 'yan cirani.

Shugaban ya bayyana cewar sun gudanar da aikin samar da ruwan sha don samun riba a Arewa maso Gabashin Najeriya da kuma rabon wata na'urar binciken cututtuka a tsakanin kananan yara a Sudan ta Kudu, ayyukan da suka taimaki al'ummar yankunan da kudaden shiga da kuma abin yi.

Daga cikin 'yan kasuwar da suka halarci taron na Legas akwai Tony Elumelu guda cikin attajiran Najeriyar wanda ya yabawa wannan yunkuri na kungiyar agajin tare da jan hankalin kamfanoni su dubi wannan shiri a matsayin hanyar juya kudade.