1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU ta fitar da matsaya kan dan jaridar Saudiyya

Yusuf Bala Nayaya
October 9, 2018

Kungiyar Tarayyar Turai ta bi sahu na kasa da kasa wajen ganin Saudiyya ta ba da bayanai dalla-dalla kan yadda dan jaridar kasar ya bace a ofishin jakadancin na Saudiyya da ke a birnin Istanbul.

https://p.dw.com/p/36E7z
Luxemburg Treffen EU-Außenminister Federica Mogherini
Hoto: Getty Images/AFP/J. Thys

Jagorar harkokin kasashen waje daga Kungiyar EU Federica Mogherini ta bayyana bukatar ba da bayanan dan taridar ga taron manema labarai a wannan Talata bayan tambayarta kan batun na bacewar ta Jamal Khashoggi.

Ta ce "A kan wannan muna tare 100 bisa 100 da Amirka, kamar yadda sakatare Pompeo ya bayyana ne sa'oi da suka gabata, muna so mu gani mahukuntan na Saudiyya sun gudanar da cikkaen bincike ba tare da wata rufa-rufa ba kan wannan batu."

Ofishin kare hakkin bil Adama na MDD ma dai ya yi kira na gudanar da binciken hadin gwiwa tsakanin kasashen na Turkiyya da Saudiyya. Wanda kuma rahotanni da ke fita sun nunar da cewa Saudiyyar ta gayyaci Turkiyya kan wannan bincike na dalilan bacewar ta dan jarida Jamal Khashoggi wanda wasu rahotanni ke zargin an halaka shi a ofishin jakadancin na Saudiyya.