1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar EU za ta kara wa'adin dakarunta a Mali

February 20, 2014

Kungiyar Tarayyar Turai ta ce za ta kara wa'adin ayyukan dakarunta dake horas da sojojin kasar Mali har ya zuwa shekarar 2016.

https://p.dw.com/p/1BBsZ
Hoto: Georges Gobet/AFP/Getty Images

Shugaban Majalisar Tarayyar Turai Herman Van Rompuy da ke wata ziyarar aiki a kasar ta Mali ce ya tabbatar da wannan labari.

Rompuy ya kara da cewa suna duba yiwuwar kara aike da wata tawaga ta kwararru fararan hula, domin bai wa jami'an tsaron da ke sauran sassan kasar horo, jim kadan bayan da ya gana da shugaban Mali Ibrahim Boubacar Keita, inda ya ce ya tattauna da shugaban kasar ne kan batun fadada bayar da horon ya zuwa jami'an tsaron 'yan sanda, da sauran masu tsaron lafiyar kasa.

Akalla dai dakarun Tarayyar Turai guda dari biyar ne, ke aikin bayar da horo ga sojojin kasar ta Mali yau da shekara guda, a garin Koulikoro da ke a nisan kilomita akalla 50 da Bamako babban birnin kasari.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita: Mohammad Nasiru Awal