1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar IS ta kara kashe wani dan Amirka

November 16, 2014

Kungiyar ta'addanci ta IS da ta addabi kasashen Iraki da Siriya ta saki wani sabon faifain bediyo da ke nuna wani dan Amirka Peter Kassig da ta yi ikirarin kashewa.

https://p.dw.com/p/1DoKJ
Hoto: picture-alliance/AP/Kassig Family

A faifain bidiyo, an nuno hoton wani dan kungiyar ta IS sanye da bakaken kaya wanda ya rufe fuskarsa dauke da yankakken kan mutum da kuma gangar jiki kwance cikin jini a gabansa, wadda ya ce ta Kassig ce.

Jami'in ba da agajin dan asalin kasar Amirka Peter Kassig wanda ya sauya sunansa zuwa Abdul-Rahman Kassig bayan ya karbi addinin Musulunci, 'yan ta'addan IS din sun sace shi ne a kasar Siriya cikin watan Oktoban shekarar da ta gabata ta 2013. Ma'aikatar tsaron Amirka ta bayyana cewa ta na aiki domin tabbatar da sahihancin faifain bidiyo da 'yan IS din suka saki.

A hannu guda kuma Firaminstan Birtaniya David Cameron ya yi tir da kisan Abdul-Rahman Kassig da 'yan ta'addan IS din suka yi wanda ya ce ya matukar firgitashi.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mohamadou Awal Balarabe