1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar kare hakkokin yan jarida ta dunia CPJ ta kiri gwamnatin Ethiopia ta yi belin yar jaridar da ta kama

January 31, 2006
https://p.dw.com/p/Bv9y

Kungiyar kare hakokin yan jarida ta dunia ,CPJ ta yi kira ga gwamnatin kasar Ehtiopia, da ta yi belin Freser Negash,wakiliyar shafin Internet, Ethiopian Review da ta ka capke tun ranar juma´a da ta wuce, a birnin Addis Ababa.

Sanarwar ta ce ,Negash itace cikamakon yan jarida, na 16, da yanzu haka su ke tsare a gidagen kurkuku a kasar Ethiopia.

Gwamnati na zargin wannan yar jarida da bata masa suna.

Cemma nan da kwanaki 10, da su ka gabata gwamnati,Ethiopia, ta koro wakilin kamapanin dullancin labarun Associated Press na Amurika daga kasar ta, wand ata zarga da rubuta kalamomi batanci.