1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar Tarayyar Afirka za ta gana kan Burkina Faso

November 3, 2014

Ana ci gaba da samun rudani kan shugabancin kasar Burkina Faso sakamakon kakkange madafun iko da sojojin kasar suka yi.

https://p.dw.com/p/1DfuQ
Hoto: Issouf Sanogo/AFP/Getty Images

Jami'an tsaron kasar Burkina Faso sun yi amfani da karfi wajen tarwatsa masu zanga-zanga a wannan Lahadin da ta gabata, sannan suka mamaye tashar talabijin ta kasa.

Masu zanga-zangar suna nuna adawa da yadda sojoji suka karbe karagar mulkin kasar bayan da Shugaba Blaise Compaore ya ajiye madafun iko ba girma ba arziki, lokacin da ya yi yunkurin sauya kundin tsarin mulki domin tsawaita wa'adin mulkinsa na shekaru 27.

Kasashen duniya na ci gaba da matsa lamba wa sojoji da suka kwace madafun iko kasar domin mutunta kundin tsarin mulki, kuma a wannan Litinin kungiyar Tarayyar Afirka za ta tattauna kan halin da ake ciki a kasar ta Burkina Faso da ke yankin yammacin Afirka, inda Kanar Yacouba Isaac Zida ya ayyana kansa a matsayin shugaban gwamnatin wucin gadi.

Wani kakain soji ya ce a shirye suke wajen mika kafa gwamnatin hadaka.

Mwallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe