1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kurar rikici ba ta lafa ba a Juba da Bangui

December 27, 2013

Yayin da ake kokarin shiga tsakani don yin sulhu a Sudan ta Kudu a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya an yi bikin Kirsmetti ne cikin tashe-tashen hankula.

https://p.dw.com/p/1AhRH
Hoto: Reuters

To a wannan makon ma jaridun na Jamus sun fi mayar da hankali ne a kan rikice-rikicen da ake fama da su a kasashen Sudan ta Kudu da kuma Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. A babban labarinta jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung cewa ta yi:

"Kusan makonni biyu da barkewar mummunan rikici a Sudan ta Kudu, an fara wata tattaunawa da nufin kawo karshen tashin hankalin. A babban birnin kasar Juba shugaba Salva Kiir ya tattauna da shugaban Kenya Uhuru Kenyatta da Firaministan Habasha Hailemariam Desalegn a wani yunkuri na yin sulhu. Ko da yake abokin gabar Salva Kiir kuma tsohon mataimakin shugaban kasar, Riek Machar bai halarci zauren taron ba, amma a wata hira da aka yi da shi ya nuna shirin zama kan teburin sulhu, matukar za a yi taron ne a Addis Ababa babban birnin kasar Habasha. A kuma halin da ake ciki babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya sake yin kira ga masu rikici da juna da su nemo hanyar magance rikicin cikin lumana."

Äthiopiens Premierminister Hailemariam Desalegn, Südsudan Salva Kiir und Präsident Kenias Präsident Uhuru Kenyatta
Hoto: picture-alliance/dpa

Shiga tsakani don yin sulhu

Kasashe makwabta na shiga tsakani don yin sulhu a rikicin Sudan ta Kudu sannan Majalisar Dinkin Duniya ta amince da kara yawan dakarunta a kasar, inji jaridar Süddeutsche Zeitung.

"A ranar Alhamis an yi wata tattaunawa a Juba babban birnin Sudan ta Kudu da zumar gano bakin zaren warware rikicin kasar. Shugaba Salva Kiir da shugaban Kenya Uhuru Kenyatta da kuma Firaministan Habasha Hailemariam Desalegn suka gudanar da taron ba tare da jagoran 'yan tawayen Sudan ta Kudu ba, Riek Machar. Wannan taro ya zo ne yayin da Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya amince da tura karin sojojin wanzar da zaman lafiya kimanin 5000 don ba da kariya ga fararen hula wadanda suka nemi mafaka a sansanonin Majalisar Dinkin Duniya da ke kasar."

Kirsmetti cikin tashe-tashen hankula

Ita kuwa jaridar Neues Deutschland tsokaci ta yi a kan rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Zentralafrika Unruhe Protest am 23.12.2013
Hoto: MIGUEL MEDINA/AFP/Getty Images

"Hatta a lokacin hutun bukukuwan Kirsmetti ma Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta ci gaba da fama da tashe-tashen hankula. Baya ga musayar wuta da aka yi tsakanin sojojin Burundi da na Cadi, a tsakiyar wannan mako an kuma yi bata-kashi tsakanin dakarun Cadi da sojojin sa kai na Anti-Balaka wadanda tun a cikin watan Satumba suke yaki da 'yan tawayen Seleka, abin da ya yi sanadiyar mutuwar sojojin Cadi shida. Jaridar ta ci gaba da cewa fadan da ake yi don kwatar mulki a birnin Bangui ya fi shafan fararen hula da ba su san hawa ba ba su san sauka ba. Yayin da shugaban gwamnatin rikon kwarya Michel Djotodia da hambararren shugaba Francois Bozize ke cusa gaba a tsakanin al'umma, yunwa ce ta addabi mutane yayin da akasari ke mutuwa sakamakon kamuwa da wasu cututtuka."

Hukunci mai tsanani ga 'yan luwadi a Yuganda

Uganda Präsident Yoweri Kaguta
Shugaban Yuganda Yoweri MuseveniHoto: Imago

Dokar hukunci mai tsanani ga 'yan luwadi inji jaridar Die Tageszeitung tana mai nuni da wani kuduri da 'yan majalisar dokokin Yuganda suka zartas wanda ya tanadi hukuncin da ka iya kai daurin rai da rai a gidan kaso a kan 'yan luwadi da madigo a kasar. Dokar ba ta fara aiki ba har sai ta samu amincewar shugaban kasar Yoweri Museveni, wanda bisa kundin tsarin mulki yana da wata guda kafin ya sanya mata hannu. Sai dai Firaminista Amama Mbabazi ya nuna shakku ga kudurin dokar da cewa yawan wakilai da ke majalisa a lokacin zartas da kudurin bai taka kara ya karya ba."

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu