1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kurdawa na amfana daga rikicin Iraki

June 19, 2014

Ficcewar dakarun Iraki daga Kirkuk, daya daga cikin yankunan da ke da arzikin man fetur ya baiwa Kurdawa damar cika burinsu na kara arzikin man da suka mallaka

https://p.dw.com/p/1CM1v
Kurdische Sicherheitskräfte bei Kirkuk 11.06.2014
Hoto: Reuters

Yankin Kurdustan da ke da kwarya kwaryan 'yancin kai a kasar Iraki, wanda kuma ya jima yana hankoran samun kaso mai tsoka daga man fetir din da ake fitarwa daga cikinsa, na amfana da hare-haren da ISIS ke kaiwa kan dakarun gwamnatin kasar.

Kundin tsarin mulkin kasar ta Iraki dai, ya bawa dakarun sojin Kurdawa da ake kira Bashmarka, damar ba da tsaro a yankin kurdawan da ke da kwarya kwaryar gashin kai, tare da hadin guiwa da dakarun gwamnatin tarayya, sai dai a yan kwanakin nan, dakarun na kurdawa sun yi ta kokarin baza ikonsu a yankunan da basa karkashin ikonsu, wadanda ke Arewa Maso Yamman kasar.

Cikin wuraren da su ka mamaye harda garin Karkuk mai dimbin arzikin man fetir, bayan da dakarun gwamnatin Iraki su ka janye daga cikinsa, don kaucewa farmakin da mayakan ISIS dake neman baza ikonsu a yankin ke kai musu.

Shallal Abdul,dan majalisar yankin na kurdawa ne, bayyana dalilin day a sanya dakarun na kurdawa suke baza ikonsu a yankunan dake karkashin gwamnatin tarayya ta Iraqi;

Gefechte in Kirkuk 12.6.2014
Dakarun Kurdawa a KirkukHoto: picture-alliance/dpa

"Bayan rugurgujewar dakarun sojin Iraqi dake bawa wadan nan yankuna kariya,ya zama wajibi mu cike gibin tabarbarewar tsaro a yankunan da baza sojojinmu a cikinsu,don kare rayuka da kadarori mallakar kurdawa da sauran yan Iraqi,don kuma hana yan ta,adda mayakan ISIS baza ikonsu a yankunanmu,domin ita kanta Bagdaza a yanzu takanta take."

Kurdawa sun fara cimma burin da su ka dade suna mafarki

Wannan janyewar da dakarun gwamnatin na Iraki ke yi, ya bawa kurdawan damar cimma burin da suka jima suna mafarkinsa, wato karin kason arzikin man fetir da ake basu daga kaso 17 zuwa 25, yadda a wannan makon, su kai gaban kansu suka fara sayarwa kasar Turkiya da wannan kaso na man fetir,suna masu shan alwashin ci gaba da rike rijiyoyin man fetir din da basu kariya da kuma ci gaba da kwason wannan sabon kason da suka bawa kansu,kamar yadda Ashti Hurami,ministan harkokin man fetir na yankin kurdawan ke fadi;

"Mu a ta bangaranmu,mun yi mutukar kintsawa don bawa rijiyoyin man nan kariya,ta hanyar tona ramukan da sojojin kundun bala zasu kai harin kar ta kwana,da dasa bama bamai a kewanyansu,don hana yan ta,adda shigowa cikinsu da makamai."

Wasu daga cikin sojojin na kurdawa da suka ja daga a garin na kurkuk mai arzikin man fetir dai, sun ce ai dama can yankin mallakarsu ne

"Dakarun kurdawa na Bashmarka suke mamaye da illahirin garin kurkuk da adama can mallakar yankin kurdustan ne akai mana karfafa karfa,kuma muda barinsa sai dai a bakin ran mu."

Mawallafi: Mahmud Yaya Azare
Edita: Pinado Abdu Waba