1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kurdawan Iraki sun bukaci da a ba su makaman zamani

Mohammad Nasiru AwalSeptember 25, 2014

Shugaban Kurdawan Massud Barzani ya bayyana haka bayan tattaunawa da ministar tsaron Jamus Ursula von der Leyen wadda ta kai ziyarar ba-zata a Iraki.

https://p.dw.com/p/1DL2s
Ursula von der Leyen mit Massud Barzani 25.09.2014 Erbil
Hoto: picture-alliance/AP Photo/Maja Hitij

Kurdawa a Iraki sun bukaci gamaiyar kasa da kasa ta ba su karin makamai kuma na zamani a yakin da suke yi da 'yan ta'addan kungiyar IS da ke fafatukar kafa daular Musulunci. Bayan wata tattaunawa da ya yi da ministar tsaron Jamus Ursula von der Leyen wadda a wannan Alhamis ta kai ziyarar ba-zata arewacin Iraki, shugaban Kurdawa Massud Barzani ya ce matukar mayakan Kurdawa na Peshmerga suka samu wadannan makamai na zamani, to ba bu wata bukatar neman karin tallafi a yakin da suke yi da 'yan IS. Ba da jimawa ba ne dai ayarin farko na makaman da Jamus ta alkawarta wa Kurdawan, za su isa yankin. Sannan sojojin rundunar Jamus za su horas da mayakan Kurdawan yadda za su sarrafa wadannan makamai.