1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kuri'a kan yarjejeniyar Brexit a Birtaniya

Mohammad Nasiru Awal LMJ
January 7, 2019

A tsakiyar watan Janerun nan majalisar dokokin Birtaniya za ta kada kuri'a kan yarjejeniyar fcewar kasar daga kungiyar EU.

https://p.dw.com/p/3B90f
Europa Theresa May EU Union Jack Flagge
Hoto: Reuters/F. Lenoir

Kafafan yada labarun Birtaniya sun ce a ranar 15 ga watan nan na Janeru majalisar dokokin kasar za ta kada kuri'a kan yarjejeniyar ficewar kasar daga kungiyar tarayar Turai EU wato Brexit. Sai dai kawo yanzu gwamnati ba ta tabbatar da wannan labari a hukumance ba.

Da tun a cikin watan Disamba da ya gabata ya kamata majalisar dokokin ta kada kuri'a kan yarjejeniyar ta Brexit, amma Firaminista Theresa May ta dage gudanar da kuri'ar, bayan ya bayyana fili cewa za ta sha mummunan kaye kan yarjejeniyar.

Daftarin yarjejeniyar kan Brexit da Firaminista May ta cimmawa da shugabannin kungiyar EU na cin karo da mummunar adawa a majalisar dokokin kasar ta Birtaniya.