1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kurz ya samu narasa a zaben Austriya

Abdul-raheem Hassan
October 15, 2017

Sakamakon farko na zaben kasar Austriya na nuna cewa jam'iyar Conservertive ta 'yan ra'ayin mazan jiya wanda Sebastian Kurz ke jagoranta ta samu nasara da kashi 30.5 cikin dari a zaben majalisar dokoki da aka yi.

https://p.dw.com/p/2ls3y
Österreich Parlamentswahl Sebastian Kurz
Hoto: Reuters/L. Foeger

Hasashen alkaluman sakamakon zaben na wucin gadi wanda kafar yada labaran kasar ORF ta wallafa a dazu na cewa jam'iyar 'yan ra'ayin rikau ce ta zo ta biyu da kashi 26.8 cikin dari. Idan dai sakamakon ya tabbata, Sebastian Kurz mai shekaru 31 da haihuwa zai kasance cikin shugabanni masu karancin shekaru a duniya. Kawo yanzu dai kashi 49 cikin dari ne kadai aka sanar a hukumar zaben kasar.