1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwalambiya: Zaben raba gardama kan yarjejeniyarsulhu

October 2, 2016

Al'ummar kasar Kwalambiya suna zaben raba gardama kan yarjejeniyar zaman lafiyar da ta kawo karshen yakin basasa a kasar.

https://p.dw.com/p/2Qo9v
Kolumbien Historisches Friedensabkommen in Cartagena unterzeichnet
Hoto: Reuters/J. Vizcaino

A wannan Lahadin al'ummar Kwalambiya ke kada kuri'ar raba gardama kan amincewa da shirin zaman lafiya na kasar, abin da zai kawo karshen yakin basasa na shekaru 52 tsakanin dakarun gwamnati da 'yan awaren kungiyar FARC masu ra'ayin makisanci.

Shugaba Juan Manuel Santos ya bukaci mutanen kasar kan su amince da yarjejeniyar wadda aka shafe shekaru biyar ana tattauna ta a birnin Havana na kasar Kyuba. Muddun aka amince da yarjejeniyar 'yan tawayen za su samu afuwa, kana kungiyar 'yan tawayen da ta zama jam'iyyar siyasa za ta shiga zabukan kasar na shekara ta 2018, tare da samun wakilci na kai tsaye a majsalisar dokoki da ta wakilai na musamman guda 10 har zuwa shekara ta 2026.

Kasashen duniya sun nuna farin ciki da yarjejeniyar da ta kawo karshen rikicin na Kwalambiya, da ya kai ga mutuwar fiye da mutane 220,000 sannan wasu milyoyi suka tsere daga gidajensu.