1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwamanda ya ja sojoji tawaye a Sudan ta Kudu

Yusuf Bala Nayaya
November 7, 2017

Laftanel kanar Chan Garang aboki ga tsohon jagoran sojoji Paul Malon ya fice daga sojan kasa zuwa bangaren tawaye mafi yawan soja da suke adawa da Shugaba Kiir.

https://p.dw.com/p/2nBzI
Südsudan Panakuach - Südsudanische Soldaten
Hoto: Reuters/G. Tomasevic

Kwamandan sojoji a kasar Sudan ta Kudu ya yi kaura da kimanin sojoji 200 zuwa bangaren 'yan tawaye mafi girma a kasar, abin da ke zuwa yayin da ake nuna kowa ya isa tsakanin Shugaba Salva Kiir da tshohon shugaban rundunar sojansa.

Lutanel kanar Chan Garang aboki ga tsohon jagoran sojoji Paul Malon ya fice daga sojan kasa zuwa bangaren tawaye mafi yawan soja da suke adawa da Shugaba Kiir. Dukkanin mutanen uku daga kabilar Dinka, kowace baraka aka gani tsakaninsu na nufin barazana ga Kiir.

A watan Mayu ne dai Shugaba Kiir ya sallami Malong wanda jami'an MDD ke zargin sojansa da hannu a aikata fyade da gallaza wa al'umma da ma kisa , da fari dai Malong da ke cikin wadanda Amirka ta sanyawa takunkumi ya yi hijira zuwa Arewa kafin daga bisani ya sake komawa babban birnin kasar ta Sudan ta Kudu inda aka yi masa daurin talala agida.

Shekaru hudu na yakin basasa a kasar ta Sudan ta Kudu dai ya rarraba kan al'umma, ya jawo mutane sun yi gudun hijira da ke zama mafi girma a cikin shekaru 20, ga batu na zargin kokarin kawar da wata al'umma daga doron kasa.