1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwanaki 100 da Kenyatta ya kwashe kan madafun iko

July 18, 2013

Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta ya cika kwanaki 100 da karbar madafun ikon kasar da ke yankin gabashin Afirka.

https://p.dw.com/p/19ABa
Hoto: Reuters

Shugaban ya yi alkawura masu yawa na kyautata rayuwar mutane, abin da yasa 'yan kasar ke zaman jiran tsammani. Gwamnatin Shugaba Uhuru Kenyatta ta cika wadanda kwanaki 100 cikin gagarumin kalubalen tabbatar da alkawuran da shugaban ya dauka na kyautata rayuwar al'umma lokacin yakin neman zabe da jawabin farko lokacin da ya dauki madafun iko:

"Mun sadaukar da kai wajen bunkasa tattalin arziki domin kyaqutata rayuwar 'yan kasa."

Shugaban ya tabbatar da shirin bunkasa harkar kiwon lafiya. Samar da magani kyauta wa mata tun daga watan Yuni. Amma mutane na ci gaba da nuna dari-dari da shirin. Kawo yanzu babu wata alamar haka, wajen daukan likitoci a aiki, abin da ke kara tambayoyi bisa halin da ake ciki. Gacheke Gachihi na cikin 'yan kungiyar kare hakkin dan Adam:

Kenia Uhuru Kenyatta Vereidigung
Hoto: Reuters

"Babu wani abin da aka gani. Mutane na cikin yunwa, yayin da 'yan majalisa ke kara wa kansu albashi. Babu abin da ya sauya, mun koma gidan jiya."

A cikin 'yan makonnin da suka gabata 'yan kasar ta Kenya sun fito kan tituna domin zanga-zangar nuna rashin jin-dadi da matakin 'yan majalisar suka dauka na kara wa kansu albashi. Yanzu malaman makarantun Kenya sun kwashe makonni suna yajin aiki. Abin takaici saboda yadda Kenyatta ya bayyana shirin samar da na'ura mai kwakwalwa ga 'yan makaranta. Tun lokacin da Kenyatta da dauki madafun iko, gwamnati ta samu kudaden haraji da suka kai Euro milyan 500, amma ta ce sai zuwa karshen shekara kafin karin albashin malamai ya fara aiki. Clara Momanyi malama ce a Jami'ar Katolika ta Gabashin Afirka, da ke birnin Nairobi na Kenya:

"Mutane suna koke-koke, saboda suna son ganin sauyi. Suna damuwa Kenyatta na bukatar lokaci, a matsayinsa na shugaba yana bukar yin wani abu. Ya dace ya samu dama, domin cika alkawura da ya dauka lokacin neman zabe. Ba kawai bayan kwanaki 100 shi ke nan ba."

Tun farko gwamnati ta bayar ta shirya ba da horo wa ministoci. Shugaba Kenyatta ya yi ba zata, wajen shigar da matasa majalisar ministoci, kuma ba 'yan siyasa ba, amma masana. Duk da haka 'yan kwakwarmaya sun kalubalanci matakin, Gacheke Gachihi ya bayyana cewar:

Kenia Supreme Court Gerichtssaal Urteil technische Probleme Wahlergebnis Präsidentschaftswahlen
Hoto: Reuters

"Wadannan ba fitattun mutane ba ne. Kuma mafi yawa suna cikin wadanda suka kuntata wa tattalin arzikin kasar."

Gachihi ya ba da misali da sabon ministan makamashi Davis Chirchir, wanda a shekarun 1990 ke hukumar aikewa da wasiku da sadarwa. Wani kalubale da Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta da mataimakinsa William Ruto ke fuskanta na tuhuma a kotun duniya, kan rikicin da ya biyo bayan zaben shekara ta 2007, wanda ya faru a karshen shekarar ta 2007 zuwa farkon shekara ta 2008.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu