1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwankaso: A guji tayar da hankali a Kano

Uwais Abubakar Idris MAB
March 15, 2019

Jigon jam'iyyar PDP a Kano Rabiu Musa Kwankwaso ya bukaci da a gudanar da zaben da za a maimata a wasu yankunan jihar cikin kwanciyar hankali. Sannan ya ce a guji nuna fin karfi ta hanyar dauko na baya a mayar gaba.

https://p.dw.com/p/3F9Z4
Rabiu Musa Kwankwaso
Hoto: DW/T. Mösch

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso wanda shi ne jigo a jam'iyyar ta PDP a jihar ta Kano ya tabo batutuwa da dama a hira ta musamman a kan zaben na gwamnan jihar Kano da ma wasu jihohi biyar na Najeriya, inda hukumar zaben za ta sake maimaita zabe a wasu yankuna domin tantance wanda ya samu nasara. Ya ce bukatarsu ita ce a yi zaben cikin kwanciyar hankali domin yi wa kowa adalci, domin akasin haka ba zai yi wa kowa dadi ba a daukacin tsarin dimukuradiyyar Najeriyar.

Tun kafin wannan dai, ana ta kokarin ganin an gudanar da wannan zabe da za’a sake a jihohi shida na Najeriya cikin kwanciyar hankali, inda hukumar zaben kanta ta bayyana dalilai da suka sanya bayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba. Abin da ya sanya Barrister Mainasara Umar mai sharhi a kan al’amuran yau da kullum ya bayyana bukatar kamanta adalci.

Nigeria Akkreditierungs-Wähler
Yawan masu zabe zai iya kasancewa kalubale a zaben da za a maimata a KanoHoto: DW/Uwaisu A. Idris

Zargin tafka magudi na kara amo sosai a tsakanin manyan jam'iyyu biyu na PDP da APC a kusan dukkanin jihohin da ake fuskantar wannan batu na  maimaita zabe a wasu sassa a jihar ta Kano. Abin da ya kara daukan hankalin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, jigo a jamiyyar PDP, bisa sakamakon da aka sanar cewa tana kan gaba a zaben jihar .

A yayin da hankali jama’a ya dauku zuwa ga jihohin shida da za’a sake maimaita zaben gwamnonin wato Kano, Sokoto, Adamawa, Bauchi, Plateau da Benue, nauyi ya koma kan hukumar zaben na tabbatar da kamanta adalci ta yadda za’a wanye lafiya.