1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsamin dangantaka tsakanin kasar da sauran kasashen Afirka

Aliyu Abdullahi Imam MNA
August 13, 2019

Hare-haren da 'yan Afirka ta Kudu ke kai wa baki mazauna kasar na kokarin lalata alakar kasar da sauran kasashen duniya, lamarin da ya tilasta wa gwamnatin kasar kokarin kare abin da take yi.

https://p.dw.com/p/3NqZz
Südafrika Xenophobie Rassismus Unruhen
Hoto: Getty Images/G.Guercia

Bakin hauren da aka cafke da ke zaune a kasar Afirka ta Kudu yayin wani farmakin da aka kai a makon baya ga bakin da suka mallaki shagunan saye da sayarwa sun gurfana a kotun magistrate inda jami'an tsaron kasar suke tuhumarsu da take dokokin shige da fice na kasar.

A makon da ya gabata ne aka kai wani samame a wasu shaguna mallakin baki mazauna kasar a birnin Johannesburg, aka kame wasu daruruwa daga cikin baki 'yan asalin Afirka da ake zargin basu da takardun izinin zama kasar. 'Yan sanda na tuhumarsu da take dokokin shige da fice ta hanyar shigowa kasar ba bisa ka'ida ba. A farfajiyar kotun dai 'yan uwansu da wasu 'yan ainihin kasar ta Afirka ta Kudun sun yi zanga-zangar nuna goyon baya ga wadanda aka kama.

Festnahme von 500 undokumentierten Migranten in Johannesburg
Hoto: DW/T. Khumalo

Wadannan baki da aka kama na cikin halin firgici da damuwa. Bayan sun gurfana gaban kotun an aika su cibiyar kula da 'yan gudun hijira ta Lindela, inda daga nan za a mayar da su kasashensu na asali.

Kungiyoyi masu kare hakkin 'yan gudun hijira sun nuna matukar bacin ransu da yadda ake tozarta bakin. Sun kuma bayyana matakin a matsayin kabilanci, kiyayya, mugunta wanda kuma ya karya dokar kasa da kasa.

Hare-haren da nuna wariyar fata da 'yan Afirka ta Kudu ke yiwa baki a kasar na kokarin lalata alakar kasar da sauran kasashen duniya.

Kasancewa 'yan Najeriya na daga cikin 'yan Afirka da wannan mataki ya fi rutsawa da su, ana sa ran cewa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai kai ziyarar kasar ta Afirka ta Kudu a watan Oktoba a wani mataki na nemo bakin zaren matsalar.