1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kyuba na halartar taro da Amirka a Panama

Gazali Abdu TasawaApril 10, 2015

A ranar Jumannan ne aka bude taron koli na nahiyoyin Amirka a kasar Panama, taron da a wanann karo ya samu halartar Kyuba da ta kwashe shekaru 21 tana bijirewa.

https://p.dw.com/p/1F67X
Panama USA Kuba Treffen Außenminister John Kerry und Bruno Rodríguez in Panama City
Hoto: Reuters/U.S. State Department

A zahiri ta ke cewa an samu kyakyawan ci gaba a cikin huldar dangantakar kasar Kyuba da takwararta ta Amirka kasashe biyu da su ka share sama da shekaru 50 ba ko ga maciji a tsakaninsu musamman a dogon lokacin milkin sugaba Fidel Castro .Dangantakar kasashen biyu ta hau turbar kyautatuwa ne tun bayan da aka samu canjin shugabanni a kasashen guda biyu.Da ya ke tsokaci akan wanann batu Carl Meacham na cibiyar nazari da bincike akan dangantakar kasa da kasa da ke a birnin Washington danganta sauyin da aka samu tsakanin kasashen biyu ya yi daidai da irin canjin zamanin da aka samu a duniya.

US-Präsident Obama in Panama
Shugaba ObamaHoto: R. Arboleda/AFP/Getty Images

"Kasar Kyuba ta yau ba wanann kasa ba ce da aka sani ta zamanin yakin cacar baka.Dan haka irin zaman gabar da kasar ta yi da kasar Amirka lokacin da ta ke a matsayin 'yar lelan Tarayyar soviet zamani ne da ya zamo a yau tsohon yayi.

Yanzu haka dai shugaba Barack Obama na da masaniya kan cewa tallafin da kasar Rasha ke bai wa kasar ta Kyuba na ja da baya a ko wace rana.kuma wanann sabon yanayin dangantakar da aka shiga tsakanin kasar ta Amirka da takwararta ta Kyuba lamari ne da duniya ka iya kalla a matsayin wani sakamakon na kyakyawar siyasar huldar danganataka kasar Amirka da kasashen waje da shugaba Obama ya assasa a lokacin milkinsa.Sai dai Mark Weisbrot na wata cibiyar nazarin harakokin siyasa da tattalin arziki da ke a birnin Washington ya ce Obaman ne kadai ke cin ribar wannan tsarin siyasar harakokin kasashen wajen kasar tasa.

USA Kuba Annäherung Kerry und Rodriguez
Bruno Rodríguez da John Kerry: Ministocin harkokin wajen Kyuba da AmirkaHoto: picture-alliance/dpa/US Department of State/G. Johnson

"Ina zaton ba za a rasa samun fahimtar juna ba a tsakanin duk masu ruwa da tsaki cikin harkokin siyasar huldar kasar da kasashen waje dama a cikin gwamnati.Domin anasu tunani wanann na iya kasancewa wata hanya ko dama ta kawar da gwamantin da ke ci a yanzu a kasar ta Kyuba".

Sai dai fadar shugaban kasar ta Amirka ta ce kawo yanzu ba bu wani shiri a hakumance na ganawar shugabannin kasashen biyu a gurin wanann taro, amma akwai yiwuwar a share daya wajen taron a samu wata dama wacce shugabannin kasashen biyu ka iya haduwa dama canza yawu a tsakaninsu.