1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Aljeriya da Senegal sun kai wasan karshe na AFCON

Mouhamadou Awal Balarabe GAT
July 15, 2019

Aljeriya da Senegal sun yi nasarar kaiwa wasan karshe na gasar cin kofin kwallon kafa ta Afirka a kasar Masar bayan da suka kori Tunusiya da Najeriya a wasannin kusa da na karshe.

https://p.dw.com/p/3M6Ye

Aski ya zo gaban goshi a kokarin da kasashen Afirka ke yi na neman lashe kofin kwallon kafa na wannan nahiya, inda bayan tankade da rairaya Senegal da kuma Aljeriya suka kai bantensu zuwa zagayen karshe. Ita dai kungiyar kwallon kafa ta Senegal ta yi nasarar yin waje rod da Tunisiya bayan da ta doke ta da ci daya mai ban haushi a yayinda Aljeriya ta doke Najeriya. A ranar Jumma'a ne za a buga wasan na karshe tsakanin Alejriya da ke neman lashe kofin a karo na biyu da kuma Senegal da ke neman lashe kofin a karon farko cikin tarihinta.