1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Laberiya: Shugaba Weah ya sha rantsuwar kama aiki

Yusuf Bala Nayaya GAT
January 22, 2018

Sabon shugaban Laberiya George Weah ya yi rantsuwar kama aiki a wannan Litinin, da kuma ke zama shugaba na farko da ya karbi mulki daga wata gwamnatin demokradiyya a tarihin kasar tun daga shekarar 1944.

https://p.dw.com/p/2rKcA
Liberia Wahlen George Weah
Hoto: picture alliance/dpa/epa/A. Jallanzo

Shahararren dan wasan kwallon kafar nan a duniya George Weah ya yi rantsuwar kama aiki a matsayin sabon shugaban kasar Laberiya a wannan rana ta Litinin, matakin da ya sanya shugaban ya zama na farko da ya karbi mulki daga wata gwamnatin demokradiyya zuwa wata a tarihin kasar tun daga shekarar 1944.

Sabon Shugaba Weah dan shekaru 51 ya karbi mulki daga tsohuwar shugaba da ta samu lambar yabo ta zaman lafiya Ellen Johnson Sirleaf, wacce ta jagoranci kasar tsawon shekaru 12 wadanda kafin su kasar ta ga kwaramniya ta yakin basasa. Weah ya sha rantsuwar kama aiki gaban shugaban kotun koli a Laberiya Francis Korkpor a babban filin wasa na kusa da birnin Monrovia.

Manyan baki da suka shaida rantsuwar sun hada da shugabannin kasashen Gabon da Ghana da Saliyo da wasu manyan abokai a fagen kwallon kafarsa kamar Samuel Eto'o daga Kamaru. Bayan rantsuwar dai Weah ya ce shekarunsa da dama sun tafi a filin kwallo, amma yanzu yana ji tamkar ba kamarshi wajen godiya ga Sirleaf da ta share masa hanya aka samu zaman lafiya. Babban kalubale da ke gabansa na zama samar da ayyukan yi ga biyan ma'aikata albashi da ba da karfin gwiwa ga 'yan kasuwa masu zaman kansu, sannan uwa uba yaki da cin hanci da rashawa a kasar da ke zama cikin matalauta mai mataki na 177 cikin kasashe188 kamar yadda shirin raya kasa na Majalisar Dinkin Duniya ya nunar. Don haka batun raya kasa na kan gaba a cewar Weah:

Liberia George Weah als Präsident vereidigt
Shugaba Weah da tsohuwar shugabar Laberiya Ellen Johson Sirleaf a bikin kaddamar da shi.Hoto: Reuters/T. Gouegnon

"Za mu samar da hanyoyi, zirga-zirga ta yi sauki, aiyukan gona su bunkasa saboda haka samar da hanyoyi na da muhimmanci."

A cewar Shugaba Weah dai wannan nasara ba za ta samu ba face al'umma ta mara wa gwamnatinsa baya musamman a fage na yaki da cin hanci da rashawa da
ake masa kallo a matsayin matsalar da ke yi wa Laberiya dabaibayi kamar yadda Musa Bamba, babban sakatare na majalisar tuntuba tsakanin addinai a Laberiya ke karin haske:

"Idan muna son zaman lafiya ba kawai a Laberiya ba har daukacin kasashen Afirka ya zama dole mu yi yaki da cin hanci da rashawa, dole shugabannin addinai a masallatai da coci-coci su tashi su yaki cin hanci da rashawa kasancewar shugabannin na zuwa wajensu. Idan malamai na addini za su yi shelar yaki da talauci a bakunansu, sannan su tabbatar al'umma na aiwatarwa to za a kori talauci a zauna lafiya."


Da dama dai masoyan George Weah na ganin zabinsa shi ne makoma mai kyau ga Laberiya kamar yadda Anvinor Sahw mazaunin Monrovia ke cewa:

George Weah
George Weah kenan a lokacin da yake taka wa AC Milan ta Italiya leda.Hoto: picture-alliance/AP Photo/C. Fumagalli

"Kamar yadda muke ji ne a hakikanin gaskiya mutane su ne shugabanci, don haka dole mu mara masa baya domin mun amince wannan shugabanci ne na al'umma."

Ita ma dai Katherine Brown cewa ta yi ta zo taron rantsar da shugaban ne saboda tana kallon sa a matsayin wakilin talakawa:

"Na zo nan ne saboda ina kaunar sa saboda nuna damuwarsa ga talakawa, saboda kasata, na amince cewa zai yi abubuwa da yawa don haka nake tare da shi tun a shekarar 2014."

George Weah dan marasa galihu dai ya kai kololuwar mataki na shuganaci a Laberiya ya taka muhimmiyar rawa a fagen kwallon duniya a shekarun 1990 da ta kai shi ga daga lambar Ballon d'Or da hukumar da ke tsara wasanni a duniya FIFA ta ba shi dan Afirka tilo da ya kai ga matakin.