1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Lafiya Jari: Illar turakun kafofin sadarwa

Abdourahamane Hassane
April 5, 2019

Turaku ko Antenna Systems a Turance na hanyoyin sadarwa na wayar hannu GSM da ake kakkafawa a tsakiyyar gari na tattare da illa ta radiation da ke iya shiga jikin dan Adam da zama cututtuka.

https://p.dw.com/p/3GNKL
Mobile Basisstation
Hoto: Colourbox

Wasu masana sun ce samar da hanyoyi na sadarwa ta hanyar GSM ci gaba ne sosai, wasu kuma na gani akwai koma baya hasali ma a kan sha'anin kiwon lafiya dangane da kakkafa turaku na GSM a duniya kamar yadda Injiniya Haruna Abubakar Lere ya bayyana cewa sinadarin da ke fita da ake kira na radiation a Turance na turakun GSM kan ratsa jikin dan Adam, hakan kuma babbar matsala ce.

Likitoci dai sun yi amannar cewar turakun suna da mummunar illa ga rayuwar dan Adam a tsawon lokacin, idan ana shakar iska za a iya kamuwa da cututtuka kana mace mai juna biyu za ta iya yin bari ma, ko kamuwa da wasu cutukan irinsu ciwon kansa na jini.

Dakta Hassan Ibarahim kwararran likita daga Najeriya ya ce girka turakun na GSM ko a cikin gidajen jama'a ko cikin unguwannin babban hadari ne. Sai dai injiniya Haruna Abubakar Lere ya ce kamfanonin na yin amfanin da makudan kudade wajen sayen gidajen jama’a kuma ba tare da yin la’akari ba da ilar ba, sai su amince.

A karshe Dakta Usman Dan Ladi ya yi kira ga hukumomi wajen daukar mataki a game da wannan al'amari. Don jin karin bayani sai a latsa shirin na Lafiya Jari na saurare a kasa.