1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masu fama da matsalar rashin gani

Ahmed Salisu AAI
August 16, 2019

Shirin a wannan makon zai duba matsalar rashin gani ne da wasu jama'a ke fama da ita musamman ma idan abu yana nesa.

https://p.dw.com/p/3O2V2
Afrika Ein Dollar Brille
Yaro mai fama da matsalar ganin abin da ke nesaHoto: Onedollarglasses/M. Aufmuth

Matsalar rashin gani na da yawan gaske, guda daga cikinsu kuwa ita ce wacce mutum kan gaza ganin abin da ke nesa duk kuwa da cewar wannan abu a bayyane yake. To dai masana kiwon lafiya sun ce akwai tarin matsalalolin da masu wannan larura kan fuskanta. Ko wane dalili ne ke haifar da wannan matsalar? Karin hasken da Rayyanu Hashim Arabi, wani kwararren likitan idanu a jihar Kadunan Najeriya ya yi kenan kan tushen wannan matsala.