1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nahiyar Turai ta fuskanci zafi mai tsanani

Zainab Mohammed Abubakar
July 12, 2019

Nahiyar Turai ta fuskanci yanayin zafi mai tsanani na shekaru 15 cikin shekaru 500 da suka gabata. Ko wannensu ya kasance mai hadari ga rayuwar jama'a a nahiyar.

https://p.dw.com/p/3Lzlq
Bildergalerie Hitzewelle in Europa Schweiz
Hoto: picture-alliance/dpa/V. Flauraud

Shekara ta 2003 ta kasance mafi tsananin zafi a Turai inda mutane sama da dubu 70 suka ce rasu sakamakon tsananin zafi, kana a 2010 wasu mutanen dubu 56 suka rasu a kasar Rasha kadai, sakamakon matsanancin zafi.

Shin yaya yanayin zafin ya kasancewa baki 'yan Afirka da suka tsinci kansu a wannan nahiya? duk da cewar a akasarin kasashen na Afirka ana fuskantar zafi?

Duk da cewar a yanzu haka ya kamata a ce damuna ta kankama a yawancin kasashen Afirka, rahotanni na nuni da cewar har yanzu wasu yankuna na fama da karancin ruwa da wani irin yanayi na zafi da rana mara misaltuwa. Illela da ke cikin jihar Kebbi wanda kuma ke kusa da kan iyakar Janhuriyar Nijar na daya daga cikin wuraren da aka fuskanci irin wannan yanayi na zafi kamar yadda Auwal Abubakar ya shaidar.

A cewar Mahamadu Rabilu Salisu da aka fi sani da suna dan matashin Amfani, a kullum idan damina tazo akan ce zafi zai tafi saboda sanyin daminar, sai dai a wannan karon ba haka ba ne.

A bara ma dai haka lamarin ya kasance, wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane wajen 700 a Sweden, da sama da 250 a Denmark, dukkan wadannan kasashe ne da basu taba tunanin cewar rana irin wannan zata zo da za su nemi na'urarar sanyaya gida da aka fi sani da suna Air Conditiner ko kuma AC ba, har sai da suka tsinci kansu cikin wannan yanayi na matsanancin zafi da ake dangantawa da sauyin yanayi.